APC da INEC sun yi mana magudi a Ondo — PDP

PDP
Bayanan hoto,

Jam'iyyar PDP ta zama mai adawa a Najeriya

Jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta ce ba ta amince da sakamakon zaben da aka gudanar a jihar Ondo, a karshen makon nan ba.

Jam'iyyar ta kuma zargi Hukumar Zaben Kasar, INEC da hada baki da jam'iyya mai mulki ta APC, a inda PDP ta nemi INEC da ta soke zaben.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam'iyyar ta PDP, Prince Dayo Adeyeye, ya fitar, PDP ta ce " sakamakon zaben da wakilin Hukumar Zabe ta INEC, farfesa Abdul-Ganiyu Ambali, ya fitar, yaudara ce sannan kuma bai dace da abun da al'ummar jihar Ondo suka zaba ba".

Sai dai tuntuni hukumar ta INEC ta nesanta kanta daga zarge-zarge irin wanda PDP take yi.

A ranar Lahadi ne dai INEC ta bayyana dan takarar jam'iyyar APC, Rotimi Akeredelu, a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Ondo.

Mista Dayo ya kara da cewa " abu ne a fili yadda 'yan jam'iyyar APC suka rinka sayen katin zaben mutane a gaban jami'an tsaro".

Daman dai jam'iyyar ta PDP ta yi ta kira ga INEC da ta dage zaben da mako biyu domin sabon dan takararta ya samu zarafin yin kamfe.

A ranar Laraba ne dai kotun daukaka kara, ta ce Eyitayo Jegede na bangaren Ahmed Makarfi ne ya cancanci tsayawa takara, ba Jimoh Ibrahim ba, na bangaren Ali Modu Sheriff.