Dylann Roof zai kare kansa a kotu

'Yan uwan mutanen da Dylann Roof ya kashe sun ce sun yafe masa
Matashin nan farar fata dan kasar Amurka da ya harbe bakar fata tara a wata coci da ke South Carolina, ya ce, yana son kare kansa a gaban kuliya.
Mai shari'a Richard Gergel, ya ce bukatar Dylann Roof ta ya zama lauyan kansa da kansa bai dace ba amma kuma an amince masa da hakan.
A watan Yunin 2015 ne dai Roof, mai shekara 22, ya harbe wasu masu bauta a coci guda 9.
Matashin yana fuskantar tuhume-tuhume guda 33 da suka hada da laifin nuna tsanar wani jinsi.
Wasu daga cikin mutanen da Dylann Roof ya harbe