CAR: Ana fuskantar barazanar karancin abinci

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin al'ummar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na fuskantar barazanar karancin abinci inda suke bukatar taimako.

Babban Jami'i hukumar Majalisar mai kula da ayyukan jin kai, Fabrizio Hochschild ya ce kashi 40 cikin 100 na kananan yara da basu wuce shekaru uku ba sun kanjame sakamakon rashin abinci mai gini jiki.

A bangare guda kuma Musulmai da Kiristoci na ci gaba da kaddamar da hare hare a kasar sakamakon yakin ba-sa-sa daya barke tun a shekarar 2013.

A farkon wannan watan ne masu bada tallafi suka alkawarin bada fiye da dala biliyan biyu don taimaka wa kasar ta farfado, sai dai Majalisar ta ce kasar na bukatar karin kudade don ciyar da jama'a dake fama da yunwa.