"Babu shaidar an tafka magudi a zaben Trump"

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai dai sun yi watsi da ikirarin da Mr Trump ya yi cewa akwai miliyoyin mutane da suka kada haramtattun kuri'u
Fadar White House ta ce babu wata shaida data nuna cewa an tafka gagarumin magudi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba.
A ranar lahadi ne Donald Trump wanda ya lashe zaben amma kuma ba shi ne yafi samun yawan kuri'a ba, ya ce akwai miliyoyin mutane da suka kada haramtattun kuri'u, koda yake bai bayyana hujjojin sa na wannan ikirari ba.
Jami'ai dai sun yi watsi da ikirarin da Mr Trump din ya yi, sai dai rahotanni sun ce 'yar takarar Jam'iyyar Green Party, Jill Stein ta mika a hukumance bukatar neman a sake kidaya kuri'un a jihar Pennsylvania.
Jami'an zabe a jihar dai sun ce ba wata shaida data nuna cewa an tafka kura-kurai, yayin da a makon daya gabata ma Ms Stein ta bukaci a sake kidaya kuri'un a Wisconsin.
Hakan na zuwa bayan da magoya bayan abokiyar karawarsa Hillary Clinton ta jam'iyar Democrat, suka ce za su goyi bayan sake kirgen kuri'u a Wisconsin.
Mrs Clinton ta samu kuri'u miliyan biyu, fiye da Mr Trump a zaben gama gari.
Amma kuma Mr Trump ya yi zarra a adadin kuri'u 270 na babbar mazabar da ake bukata don zama shugaban kasa.
Wannan ya dagora ne ga takarar da aka yi daga jiha-zuwa-jiha.

Trump: Miliyoyi sun kada kuri'unsu ta haramtacciyar hanya
Zababben shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce, ya samu galaba a kuri'un gama gari, baya ga miliyoyin kuri'u da jama'a suka kada ta 'haramtacciyar hanya'.