Sojin Syria sun yi nasara kan 'yan tawaye a Aleppo

Dakarun Syria na kafa tutar kasar, a yankin da suka kwato daga hannun 'yan tawaye
Bayanan hoto,

An shiga shekara ta biyar da fara yakin basasar Syria

'Yan tawayen Syria a gabashin Aleppo sun ce sun ja da baya zuwa wani wuri dake da kariya bayan dakarun gwamnati sun fatattake su daga bangaren arewaci a birnin da aka raba gida biyu.

Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce bangaren 'yan tawayen sun rasa iko da suke da shi a baya na kusan kashi 40 a yankin da suka mamaye.

Dubban fararen hula ne dai ke tserewa gumurzun da ake yi har da wadanda ke zaune a yankunan da dakarun gwamnati ke rike da su a yammacin Aleppo.

Farmakin da ake ta kaiwa a yan kwanakin nan ya yi tsanani sosai inda yasa shugaba Assad a wani matsayi na kara karfi sabanin yadda lamarin yake shekara guda rabi da ya gabata

Babban mai shiga tsakani na gamayyar 'yan adawa da kuma kungiyoyin 'yan tawaye George Sabra na kwamitin koli dake sasanta wa ya shaida wa BBC cewa koda kuwa dakarun gwamnati sun kwace daukacin birnin Aleppo, ba zai kawo karshen boren ba.