Shugabannin kasashe sun tafi makokin Fidel Castro

Marigayi Fidel Castro
Bayanan hoto,

Za a kwashe kwanaki tara ana zaman makoki a Cuba

Shugabannin kasashe daban-daban na duniya sun fara is kasar Cuba don halartar jana'izar marigayi Fidel Castro.

Wadanda tuni suka isa kasar sun hada da wasu shugabannin kasashen Latin Amruka da nahiyar Afrika da kuma wasu kasashen da ke da kyakyawar dangantaka da jagoran juyin juya halin, lokacin da suka gwagwarmayar neman yancin kai.

Kasashe kamar Burtaniya da Faransa da Canada dai zasu tura wakilan su ne don halartar jana'izar.

Sai dai Fadar White House ta tabbatar ce babu wanda zai halarci janaizar tsakanin shugaba Obama da mataimakin sa Joe Biden.

A jiya ne dubun-dubatan 'yan kasar Cuban suka yi dandazo a dandalin juyin juya hali dake birnin Havana don jimami tare da bankwana da tsahon shugaban kasar.

kafafen yada labaran kasar tun daga jaridu, da gidajen talabijin da kuma radiyo, na gabatar da shirye-shiryen alhinin mutuwar marigayi Castro.