Jirgin na dauke dan 'yan wasan kwallon kafar Brazil

Dan wasan kwallon kafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jirgin na dauke da 'yan wasan kwallon kafar Brazil

Rahotanni daga kasar Colombia na cewa wani jirgin sama dauke da fasinjoji 72 ya fado a kasar.

Jirgin ya fadi ne yayin da ya kusa da birnin Medellin.

Jirgin saman da aka yi shatar sa ya fito ne daga kasar Bolivia, kuma yana dauke ne da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Brazil -- Chapocoense.

'Yan kwallon na shirin yin wasan karshe ne da kungiyar wasa ta Atletico Nacional dake birnin Medellin.

Kawo yanzu ba a tantance wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata ba.