Burundi: Willy Nyamitwe ya tsallake rijiya da baya

Burundi Nyamitwe

Asalin hoton, AFP/Getty Image

Bayanan hoto,

Mr Nyamitwe wani mai fada a ji ne a gwamnatin Burundi

Babban mai bai wa shugaban kasar Burundi shawara Willy Nyamitwe, ya tsallake rijiya da baya, yayin wani yunkurin hallaka shi a birnin Bujumbura.

Amma kuma mahukunta sun ce daya daga cikin masu kare lafiyarsa ya mutu.

Mr Nyamitwe ya dan samu rauni a kafadarsa, yayinda daya mai tsaron lafiyarsa shima ya samu rauni a harin daren Litinin in ji hukokomi.

A bara ne kasar Burundi ta fada cikin rikicin siyasa, lokacin da shugaba Pierre Nkurunzinza ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara karo na uku.

Mutane fiye da 500 suka mutu, kana akalla 270,00 suka tsere daga kasar.