Mara ganin da 'ya fi masu ido fasaha'

Mansur ya ce babu nakasasshe sai kasasshe
Bayanan hoto,

Ibrahim Mansur wanda ya hadu da cutar makanta yana dan shekara 5

Wani matashi da ba ya gani, mai shekara 25, a garin Geza da ke yankin Murya ta jamhuriyar Niger, yana sana'ar tura kudi ta wayar salula.

Ibrahim Mansur bai tsaya nan ba kawai, yana dawo da layin wayar da ya lalace ko ya salwanta.

Bugu da kari, matashin yana aikin daukar taki zuwa gonar mutane, a amalanken shanu.

Ibrahim ya ce " duk abin da mai ido yake yi, idan na rubuta shi a zuciyata ni ma na fara wannan abu, to fa kadan mai ido zai kara a kan inda na tsaya."

Wasu mazauna Geza, garinsu Ibrahim, sun ce matashin yana yin aikin gona da suka hada da fardar gyada.

Sannan kuma ya san hagunsa da damansa saboda ba ya bata idan yana tafiya.

Wani abun mamaki ma shi ne idan har kun taba yin hannu da Ibrahim, to har abada ba zai manta da kai ba.

Ibrahim Mansur dai ya gamu da nakasar rashin gani ne yana dan shekara biyar da haihuwa, bayan fama da cutar da ke haifar da cin zazzana.