OPEC za ta yi muhawara kan rage yawan mai

OPEC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana ja-in-ja tsakanin Sadiyya da Iran

Kasashe mambobin kungiyar OPEC da ke da arzikin man fetur za su yi muhawara kan rage yawan man da suke samarwa.

Kasashen, wadanda ke taro a Vienna ranar Laraba, za su yi muhawar ce da nufin sanya farashin fetur ya tashi a kasuwannin kasashen duniya.

A watan Satumba ne kungiyar, mai mambobi 14, ta amince ta rage yawan man da take samarwa; sai dai rahotanni sun ce ana ja-in-ja tsakanin wasu kasashen kungiyar kan batun.

Kasar Saudiyya na so a rage yawan man da ake samarwa, yayin da Iran ta kafe cewa ba za ta rage nata man ba, musamman idan aka yi la'akari da cewa ba ta dade da soma fitar da man ba bayan an janye takunkumin da aka kakaba mata.

Farashin man ya yi faduwar da bai taba yi ba cikin shekaru da dama, kuma ya zuwa yanzu OPEC ba ta dauki matakin shawo kan matsalar ba.