An dakatar da karin kudin data a Nigeria

Wasu mata na amfani da wayar salula

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan Najeriya da dama sun soki matakin da gwamnati ta so dauka

Hukumar da ke sa ido a a kan kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC ta dakatar da shirinta na kara kudin data ga masu amfani da wayar salula.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Tony Ojobo ya aikewa manema labarai, ya ce sun dauki matakin ne sakamakon sukar da suke sha daga wurin jama'a.

A cewarsa, hukumar ta umarci kamfanonin sadarwa su dakatar da kara kudin datar kan masu amfani da su.

A makon jiya ne hukumar ta bai wa kamfanonin sanarwar umarnin kara kudin da suke sayar da data zuwa kwabo 90 kan kowanne mega bite daga ranar daya ga watan Disamba mai zuwa.

Sai dai 'yan Najeriya sun soki matakin, suna maus cewa wani yunkuri ne na hana su fadar albarkacin bakinsu.

Kafin a saoke karin zai shafi manyan kamfanoni ne irin su MTN da Globacom da Airtell.

Haka kuma an yi niyyar rage farashin datar da kananan kamfanoni.

A baya dai manyan kamfanonin na sayar da data a kan: Etisalat N0.94k/MB, Airtel N0.52k/MB, MTN N0.45k/MB da kuma Globacom N0.21k/MB.

Su kuma kananan kamfanoni na sayar da data a kan: Smile Communications N0.84k/MB, Spectranet N0.58k/MB da kuma NATCOMS (NTEL) N0.72k/MB.