Amnesty ta ja hankalin hukumomi a Gambia kan 'yanci lokacin zabe

Yana takara da Adama Barrow na gamayyar jam'iyyun adawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya kwashe shekaru 22 yana mulkin Gambia

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta ja hankalin hukumomi a kasar Gambia da cewa su tabbatar an yi zaben shugaban kasar na ranar Alhamis lami lafiya.

Kungiyar ta kara da cewaa tabbatar ba a tauyewa mutane hakkin fadar albarkacin bakinsu ba.

Shugaban kasar mai ci, Yahya Jammeh wanda kuma shi ma dan takara ne, ya yi kashedin cewa babu hurumin gudanar da ko da zanga-zangar lumana bayan zabe.

Da man dai ko da a watan Aprilun da ya gabata sai da aka jefa wasu fitattun 'yan adawa a kurkuku sakamakon wata zanga-zangar nuna kin jinin salon mulkin shugaban.

Yahya Jammeh yana fafatawa ne da Adama Barrow na gamayyar jam'iyyu wanda kuma za a iya cewa sabon yanka ne a siyasance.

A shekarar 1994 ne dai Yahya Jammeh ya karbi mulkin kasar, bayan wani juyin mulki da ya jagoranta.