Matasan N-Power sun ce ba su gani a ƙasa ba

Bayanan sauti

Ku saurari hirar da muka yi da wani matashi

Wasu matasan da suka samu aikin N-Power, karkashin gwamnatin tarayyar Najeriya, sun shaida wa BBC cewa gwamnati ba ta yi shirin fara aikinsu ba duk da cewa a ranar Alhamis ya kamata su soma aikin.

Sai dai sun ce suna sa ran gwamnatin za ta yi gaggawar tuntubar su domin soma aikin.

Shazali Sani, wani matashin da ya samu nasarar shiga rukunin farko da za su amfana da wannan shirin a jihar Kano, ya ce "shirin da gwamnati ta yi yana tare da ita , ba ta kai ga bayyana mana ba; kuma bayyana mana ne zai sa mu soma aiki."

Mai taimakawa mataimakin shugaban Najeriya, ofishin da ke kula da alhakin shirin samawa matasa aiki na N-Power, Hafiz Ibrahim, ya ce ba haka batun yake ba.

A cewarsa, ranar farko ta fara wannan shiri za ta zama lokacin sake tantance matasan domin gane unguwowinsu da garuruwansu, kafin daga bisani a fada musu wurin da za su je aiki.

Ya kara da cewa matasa 200,000 da aka dauka aiki ba za su fuskanci matsalar albashi ba.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Matasa na fama da rashin aiin yi a Najeriya

A watan jiya ne dai gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin sunayen matasa dubu 200 da ta ce sun samu nasarar shiga kashin farko na shirin na N-Power.

Matasa dubu 150 ne aka dauka a matsayin malaman makaranta.

Dubu 30 kuma za su yi aiki a fannin noma, yayin da ragowar dubu 20 din za su yi aiki a fannin kiwon lafiya.

Miliyoyin matasa ne dai a kasar ke fama da rashin aikin yi.

Kuma 'yan kasar sun zura ido domin ganin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari za ta shawo kan wannan matsala.

Magance matsalar aikin yi dai na daya daga cikin batutuwan da shugaba Buharin ya yi alkawarin magancewa lokacin yakin neman zabensa.

Kididdiga ta nuna cewa akwai kimanin matasa miliyan 70 daga cikin mutanen Najeriya miliyan 167.