Zaben Trump: Soyinka ya yaga katinsa na zama a Amurka

Getty Image

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Soyinka, wanda marubucin kagaggen labari da wasan kwaikwayo da wake ne, ya lashe kyautar Nobel ta adabi 1986

Dan Nigerian nan wanda ya taba lashe kyautar Nobel ta adabi, Wole Soyinka, ya ce ya cika alkawarin da ya yi, na jefar da katin shaidar zama dan Amurka idan Donald Trump ya ci zabe.

Kwanaki kadan kafin zaben ne dai Soyinka ya yi alkawarin sarayar da katinsa na zama idan Trump ya lashe zaben kasar domin nuna adawa da kamfen din da ya yi cewar zai dauki matakai masu tsauri kan 'yan gudun hijira.

Soyinka mai shekara 82, ya fada wa kamfanin dillacin labarai na AFP a wajen wani taro kan ilmi a Jami'ar Johannesburg cewar ya cika alkawarin da ya dauka, ya raba gari da Amurka.

Ya kuma kara da cewar "Ina fargabar abin da zai faru a lokacin mulkin Trump... Na jefar da katin shaidar zama na dan Amurka, na kuma dawo da zama a wurin da nake tun asali", yana nufin kasarsa Nigeria.

Soyinka, wanda marubucin kagaggen labari da wasan kwaikwayo da wake ne, ya lashe kyautar Nobel ta adabi 1986, kuma yana koyarwa a jami'o'in Amurka da suka hada da Harvard da Cornell da kuma Yale.

Soyinka wanda daya ne daga cikin 'yan Afirka da suka yi fice a rubuce-rubuce da fafutuka, an taba daure shi a 1967 inda ya yi zaman wakafi na wata 22 a lokacin yakin basasa a Nigeria.