Gambia: Yahya Jammeh zai amince da shan kaye

Asalin hoton, AFP
Yahya Jammeh ya zama shugaban kasa ne bayan wani juyin mulki a shekarar 1994
Shugaban hukumar zaben Gambia ya ce shugaban kasar Yahya Jammeh zai amince da shan kaye a zaben shugaban kasar da aka yi ranar Alhamis.
Mista Jammeh, wanda ya shafe shekara 22 a kan karagar mulki, yana kara ne da wani dan kasuwa Adama Barrow.
Shugaban hukumar zaben Alieu Momar Njie ya ce wannan ba karamin abin al'ajabi ba ne a ce shugaban na Gambia zai amince da shan kaye tun kafin a bayyana sakamakon zaben.
Asalin hoton, Reuters
Barrow na da farin-jini a wajen matasa
Har yanzu Mista Jammeh, wanda ke mataki na biyu a kuri'un da aka bayyana, bai ce komai ba game da wannan batu ba.
Sai dai ministan harkokin kasashen waje da kuma babban sifeton 'yan sandan kasar sun yi kira da a kwantar da hankali.
Shi dai Jammeh ya zama shugaban kasa ne bayan wani juyin mulki a shekarar 1994.