Watakila Amurka ta tsawaita takunkumi kan Iran

Trump

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Trump ya ce shi ba salihi ba ne

Majalisar Dattawan Amurka, ta amince da wani kudirin doka da yake son kara tsawaita takunkumi na shekaru goma, a kan kasar Iran.

Kudirin ya nemi hukunta duk wasu kamfanonin kasar ta Amurka da ke huldar sayi-in-saya da Iran.

Gwamnatin Obama dai ta ce babu bukatar sake kakabawa Iran takunkumin da ta yi fama da su.

To amma 'yan majalisar wadanda bangaren jam'iyyar Republican ne ke jagorantar su, sun ce akwai bukatar sake duba kudirin dokar.

Hakan sun ce zai ba wa shugaba mai jiran-gado, Donald Trump cikakken ikon hukunta Iran, idan ta yi tutsu wajen martaba yarjejeniyar dakatar da hada nukiliya, da aka cimma a bara.

Sharhi, Usman Minjibir

Daman dai Mista Trump, a lokacin yakin neman zabensa, ya ce zai dawo da hannun agogo baya kan yarjejeniyar da Amurka ta cimma da Iran.

To sai dai kuma a baya-bayan nan ne wani darektan Hukumar Leken Asiri ta Amurka wato CIA, ya ja kunnen Donald Trump da cewa wargaza yarjejeniyar ba karamar masifa za ta haddasa ba.

Wasu kuma na ganin cewa Mista Trump zai sauya tunaninsa kan Iran, kasancewar Iran babbar aminiyar kasar Rasha ce.

Shi kuma Donald Trump yana matukar martaba shugaban Rashar, Vladimir Putin.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya bayyana Putin da shugaban da ya fi Barack Obama na Amurka.

Hakan kuma ana ganin wani ɗanba ne na dawo da alaka tsakanin Rashar da Amurka wadda ta dade da yin tsami.

Sai dai kuma wasu na ganin barazanar da Trump yake yi wa Iran ba ta rasa nasaba da takobin da ya lasa ta goge abubuwan da Obama ya shuka.