Dole mu hana Larabawa kwarara cikin Amurka —Trump

Trump ya ce Michelle Obama bata iya komai ba sai yakin neman zabe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Trump ya ce Michelle Obama bata iya komai ba sai yakin neman zabe

Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump ya lashi takobin yin duk abin da zai iya yi wajen kankare 'yan ta'adda daga Amurka.

Ya kara da cewa "wasu mutane da ba mu san asalinsu ba suna kwararowa daga gabas ta tsakiya, saboda haka dole ne mu dakatar da su."

Mista Trump ya sake nanata batun da ya rinka yi a lokacin yakin neman zabe wato "america ce gaba da komai."

Sai dai kuma mista Trump ya yi hani dangane da kin jinin wani mutum saboda abin da ya yi imani da shi da kuma amfani da mummunan furuci ga mutane.