Mutum 100,000 na fuskantar yunwa a arewa maso gabashin Nigeria

Rikicin Boko Haram ya fi shafar mata da kananan yara
Bayanan hoto,

Rikicin Boko Haram ya fi shafar mata da kananan yara

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa fiye da mutum 100,000 na hadarin kamuwa da matsananciyar yuwan a arewa maso gabashin Najeriya.

Majalisar ta ce mutanen za su fada cikin mummunar yunwar ce sakamakon farin da ya auku saboda rashin yin noma a yankin.

Wani rahoto da majalisar ta fitar ranar Juma'a ya ce duk da yake jami'an tsaro sun kwato garuruwa da dama daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram, amma manoma ba za su iya yin aiki ba saboda fargabar sake kai musu hare-hare.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Majalisar dinkin duniya ta ce babu isassun kudin da za bai wa mutanen agaji

Majalisar ta kara da cewa kimanin mutum miliyan bakwai na matukar bukatar taimako a yankin.

Ta yi kira da a tara sama da $1bn domin kawar da abin da ta bayyana a matsayin "babban bala'in da ke addabar Afirka a halin da ake ciki."