Tarihin mai gadin da ya zama shugaban kasar Gambia

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Barrow

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Barrow na da farin-jini sosai a wajen matasa

Sabon shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, fitaccen mai saye da sayar da gidaje ne, wanda bai taba rike wani mukami na siyasa ba kafin kayen da ya yi wa Shugaba Yahya Jammeh a zaben watan Disamba.

An haife shi ne a shekarar 1965 a wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin nan na Basse a gabashin kasar.

Kafin a tsayar da Mr Barrow, mai shekara 51, a matsayin dan takarar shugaban kasar, ya kwashe sama da shekara goma yana hada-hadar gidaje.

Ya zauna a London a shekarun 2000, lokacin da yake karatu kan harkokin gidaje, kuma a lokacin ne ya yi aiki a matsayin mai gadin babban kantin nan na sayar da kaya, Argos a arewacin London.

Asalin hoton, TWITTER

Bayanan hoto,

Barrow ya c e ba zai daina kaunar Arsenal ba

A wancan lokacin ne ya soma goyon bayan kungiyar kwallon kafar Arsenal.

Ya koma kasar Gambia a shekarar 2006 inda ya soma kasuwanci a fanni gine-ginen gidaje.

A lokacin da yake yakin neman zabe, Mr Barrow ya sha sukar Shugaba Jammeh kan rashin sanya wa'adi biyu kawai ga duk wanda zai shugabanci kasar sannan ya soki daurin da aka yi wa 'yan jam'iyyun hamayya.

Mista Barrow yana fafutikar ganin bangaren shari'a ya samu 'yanci sannan 'yan jarida da kuma kungiyoyin farar-hula sun samu damar fadin albarkacin bakinsu ba tare da wata shakka ba.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Matasa sun mara wa Mista Barrow baya sosai

Ya ce zai kafa gwamnatin hadaka ta shekara uku wacce za ta kunshi jam'iyyun hamayya idan ya ci zaben.

Sabon shugaban kasar na Gambia ya ce Jammeh ba shi da imani, sannan ya sha alwashin soke dukkan shirye-shiryen da yake aiwatarwa.

Ya ce kasar za ta koma cikin kungiyar Commonwealth da kuma kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya, ICC.

Mr Barrow dai mutum ne da sai ya tauna magana kafin ya yi ta, kuma ba shi da irin zaƙin maganar nan da ke jan hankalin masu saurarensa.

Sabon shugaban na Gambia Musulmi ne wanda ke da mata biyu da 'ya'ya biyar.