Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben Gambia

Barrow

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Adama Barrow, wanda mai hada-hadar gidaje ne, na da farin-jini a wurin matasa

Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Alhamis.

Shugaban hukumar zaben Alieu Momar Njie ya bayyana dan takarar 'yan adawa Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben.

Mista Jammeh, wanda ya hau mulki a 1994, ya amince da shan kaye, a cewar shugaban hukumar zaben.

Ba a taba mika mulki a cikin ruwan sanyi a Gambia ba tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai a 1965.

Mista Njie ya ce Mista Barrow ya lashe zaben na ranar Alhamis da tazarar fiye da kuri'u 50,000.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Adama Barrow has proved popular with younger voters

Mista Jammeh, wanda ke ikirarin bin tafarkin addini sau-da-kafa ya ce "zai shafe shekara biliyan guda yana mulki idan Allah ya so".

Ya dai shafe shekara 22 a kan karagar mulkin kasar, wacce ta dogara da 'yan yawon bude ido wurin samun kudaden shiga.

Wakilin BBC a Gambia Umaru Fofana ya ce Adama Barrow yana da farin jini matuka a wurin matasa.

Wanene Adama Barrow?

Asalin hoton, AFP

  • An haifi Adama Barrow ne a shekarar 1965 a wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin nan na Basse a gabashin Gambia.
  • Ya koma birnin London a shekarun 2000, kuma wasu rahotanni sun ce ya taba yin aiki a matsayin jami'in da ke tsaron babban kantin nan na sayar da kaya, Argos a arewacin London a lokacin da yake karatu a can.
  • Ya koma kasar Gambia a shekarar 2006 inda ya koma kasuwanci a fanni gine-ginen gidaje.
  • Jam'iyyun hamayyar da suka yi hadin gwiwa ne suka tsayar da Barrow, mai shekara 51, a matsayin mutumin da zai fafata da Shugaba Jammeh.
  • Ya sha sukar rashin sanya wa'adi biyu na kujerar shugaban kasar sannan ya soki daurin da aka yi wa 'yan jam'iyyun hamayya.
  • Barrow yana fafutikar ganin bangaren shari'a ya samu 'yanci sannan 'yan jarida da kuma kungiyoyin farar-hula sun samu damar fadin albarkacin bakinsu ba tare da wata shakka ba.
  • Ya ce zai kafa gwamnatin gwamnatin hadaka ta shekara uku wacce za ta kunshi jam'iyyun hamayya idan ya ci zaben.