Malaysia ta gargadi Myanmar kan kisan Musulmi

Musulmai 'yan kabilar Rohinjya na tserewa rikicin Rakhine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Musulmai 'yan kabilar Rohinjya na tserewa rikicin Rakhine

Ma'aikatar kasashen waje ta Malaysia ta fitar da wata kakkausar sanarwa da ke fallasa irin kisan kiyashin da makwabciyarta, Myanmar ke yi wa tsirarun musulmai 'yan kabilar Rohingya.

Kasar ta Malaysia ta ja hankalin Myanmar da ta taka wa wannan mummunar dabi'a birki bisa la'akari da irin illar da take haifar wa ta fuskar jinkai.

Sai dai kuma Myanmar din ta yi gargadin cewa wahainiyar Malaysia ta kiyayi ramarta.

Amma Malaysia ta ce abin da ya sa take son yin ruwa da tsaki a al'amarin, batun jinkai ne, ba wai saboda addininsu daya da 'yan kabilar ta Rohyngya ba.

A kwanan baya ma wani babban jami'ai na majalisar dinkin duniya ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Myanmar tana yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya tsiraru kisan kare-dangi.

John McKissick na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ya ce dakarun sojin kasar dai sun yi ta kisan 'yan kabilar ta Rohingya a jihar Rakhine, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa makwabciyar kasar Bangladesh.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jami'an da ke kula da kan iyaka sun tsare Musulmin Rohingya da dama

Gwamnatin kasar dai ta kaddamar da hare-haren da ta ce na kawar da masu tayar da kayar baya ne da ke kai hare-hare a kan iyakarta tun watan Oktoba.

Ta musanta zargin da babban jami'n majalisar dinkin duniyar ya yi.

Jami'an gwamnatin sun ce 'yan kabilar ta Rohingya suna banka wuta kan gidajensu a jihar ta Rakhine domin su dora alhakin hakan kan gwamnati.

BBC ba za ta iya zuwa yankin domin tantance gaskiyar al'amari ba saboda an hana 'yan jarida da masu bayar da agaji shiga yankunan.

'Yan kasar ta Myanmar 'yan kabilar Buddha mafiya rinjaye suna yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya, wadanda suka kai miliyan daya, kallo a matsayin bakin-haure da suka shiga kasar daga Bangladesh.