'Ronaldo da Mourinho sun kauce wa biyan haraji'

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A watan jiya Ronaldo ya sanya hannu a sabon kwantaragi da Real Madrid

Rahotanni sun nuna cewa fitaccen dan wasa Real Madrid, Cristiano Ronaldo da wasu 'yan wasan sun zille wa biyan harajin miliyoyin daloli, ta hanyar boye kudadensu a kasashen da ake amfani da su don kauce wa biyan harajin.

Wani bincike da aka wallafa a mujallar Der Spiegel ta kasar Jamus ya gano hakan ne ta hanyar bayanan da aka kwarmata, cikin su har da takardun hakika na kwangilolin da 'yan wasan suka sanya wa hannu da bayanan sirrinsu da kuma sakonnin imel.

Lauyoyin Ronaldo sun ce hukumomin da ke karbar haraji na Spain sun yi bincike sosai kan takardun harajinsa kuma ba su gano wata badakala ba.

Sauran masu ruwa-da-tsaki a harkokin wasannin da ake zargi da zille wa biyan harajin sun hada da kocin Manchester United, Jose Mourinho, wanda kamar Ronaldo, yake amfani da wani wakili mai suna Jorge Mendes wajen ajiye kudinsa a kasashen da ake kauce wa biyan harajin.

Kamfanin Mr Mendes, Gestifute, ya ce Mourinho ya cika dukkan sharudan biyan haraji na kasashen Birtaniya da Spain.