Sarkin Kano ya shawarci Buhari kan cin bashin $30b

Shugaba Muhammadu Buhari tare da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari tare da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu

Mai martaba Sarkin Kano a Najeriya, Alhaji Muhammadu Sanusi ya ce kuskure ne gwamnatin kasar ta ce za ta ciwo bashin kusan dala biliyan talatin, akan cewa za ta biya bashin a cikin shekaru biyu.

Da yake jawabi a wajen wani taro a Abuja, Sarki Sanusi ya ce ciwo bashin, abu ne mai kyau, amma idan har gwamnatin za ta samu sassauci a yarjejeniyar bashin, sannan kuma a yi amfani da kudin wajen bunkasa bangaren makamashi, da lantarki da gina hanyoyi.

Sai dai Sarkin ya ce ba ya tunanin abu ne mai yiwuwa gwamnatin Najeriyar ta iya samo bashin dala biliyan talatin din a cikin shekaru biyun da suka rage mata, tun da har ta kasa samo dala biliyan biyu a shekaru biyu.

Ya ce bisa alkaluman tattalin arzikin Najeriya na yanzu, mawuyaci ne gwamnatin tarayya ta iya samo bashin kudin da take so, ko da a ce majalisar dokokin kasar ta amince mata hakan.

Alhaji Sanusi ya shawarci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya fi dora fifiko wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Ya ce hakika gwamnatin Buhari ta gaji matsaloli daga gwamnatin da ta gabata, amma kuma ba ta dauki matakan da suka dace ba na gyara kura-kuran gwamnatin da ta gabata, da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.

A baya bai, shugaban Najeriya ya ce karbo bashin dala biliyan talatin din ya na da muhimmanci saboda karancin kayan bunkasa tattalin arziki da kasar ke fama da su a dai-dai lokacin da farashin man ya fadi a kasuwannin duniya.