Amfani da siyasar ƙabilanci a Ghana

Magoya bayan jam'iyyu a Ghana kan yi shiga iri-iri a wuraren gangamin yakin neman zabe

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Magoya bayan jam'iyyu a Ghana kan yi shiga iri-iri a wuraren gangamin yakin neman zabe

Yayin da zaben kasar Ghana ke ƙara ƙaratowa, wasu 'yan kasar na nuna damuwa kan yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da ƙabilanci wajen yaƙin neman zabe.

Tuni wasu 'yan siyasar kasar suka yin tur da yakin neman zaben ta hanyar amfani da ƙabilanci.

Wasu masu sharhi dai na ganin hakan wani babban koma baya ba ne a demokradiyar kasar da ma zamantakewar jama'ar ta Ghana.

A ranar Laraba mai zuwa ne dai za a kada ƙuri'ar zaben shugaban kasar ta Ghana da 'yan majalisu.

Fafatawar neman shugabancin kasar, ya fi zafi tsakanin manyan jam'iyyun kasar guda biyu wato NDC mai mulki da kuma NPP ta adawa.

Shugaba John Dramani Mahma wanda shi ne shugaban kasar mai ci, yana neman tazarce a ƙarkashin jam'iyyar ta NDC inda ita kuma jam'iyyar NPP, ta tsaiyar da Nana Akufo-Addo domin ƙalubalantar shugaban mai ci.