'Yan kasar Italiya na zaben rabe gardama

Mr Renzi ya ce zau sauka daga kan mulki matukar ya sha kaye a zaben raba gardamar

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mr Renzi ya ce zau sauka daga kan mulki matukar ya sha kaye a zaben raba gardamar

A ranar Lahadi ne 'yan kasar Italiya za su kada ƙuri'a a zaben rabe gardamar kan sauye sauye a kundin tsarin mulkin kasar da Firai minista Matteo Renzi ya kira.

Sauye-sauyen da ake shirin yi zasu rage ƙarfin ikon Majalisar dattawan kasar tare da karawa bangaren zartarwa iko.

Mr Renzi dai ya ce zau sauka daga kan mukamin sa matukar ya kasa cimma burin sa na samun amincewar masu kada ƙuri'a a zaben raba gardamar.

Wasu shugabanni a nahiyar turai na fargabar cewa, rashin amince wa da sauye-sauyen ka iya haifar da rikicin siyasa tare da ƙara dagula al'amurra ga harkar bankunan kasar.