Gobara ta hallaka mutane a California

Mutane 9 sun mutu kuma fiye da mutum 100 ba'a ji duriyar su ba
Bayanan hoto,

Mutane 9 sun mutu kuma fiye da mutum 100 ba'a ji duriyar su ba

'Yan sanda California na fargabar cewa mai yiwuwa akwai kimanin mutane 40 da suka mutu a wata gobara data tashi a wani gidan ajiye kayayyaki da ake amfani da shi wajen shirya bukukuwa a Oakland a daren Juma'a.

An dai tabbatar da mutuwar mutane 9, sai dai akwai fiye da mutane 100 da har yanzu ba'a ji duriyar su ba.

Ray Kelly wani jami'in 'yan sanda a Oakland ya ce suna fargabar cewa akwai kananan yara da dama cikin wadanda suka mutu.

Ya ce mun samu mutane 9 da muka tabbatar sun mutu, kuma mun yi amannar akwai sauran mutane amma ba zamu bayyana adadin su ba a halin yanzu, mun samu rahotanni daga iyalai na wasu mutanen da suka bata, wasun su ma ba Amurkawa ba ne, kuma galibin mutanen da lamari ya rutsa da su matasa ne.

Wadanda suka tsira da ransu dai sun ce basu ji ?arar na'urar da ke nuna cewa hayaki na tashi ba a gidan, kuma daya daga cikin na'urorin kashe gobarar bata aiki.