Cuba: Dubban jama'a sun yi wa Fidel Castro bankwana

Dubbun-dubatan jama'a tare da wasu shugabannin ƙasashen duniya suka halarci bikin

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubbun-dubatan jama'a tare da wasu shugabannin ƙasashen duniya suka halarci bikin

Shugaban kasar Cuba Raul Castro, ya jagoranci wani buki na karshe da aka shirya don bankwana ga dan uwansa marigayi Fidel Castro.

An dai gudanar da bukin ne a birnin Santiago inda dubbun-dubatan jama'a tare da wasu shugabannin kasashen duniya suka halarta.

Shugaban kasar ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da tsarin kwaminisanci da Fidel ya jagoranta, wanda ya mutu a makon daya gabata yana da shekaru 90.

Wakilin BBC ya ce shugaban kasar ya kuma sanar wa dubban mutanen da suka taru cewa, ba za'a sanya sunan tsohon shugaban kasar a duk wasu hanyoyi ko gine-gine ba kamar dai yadda marigayin ya bukata.