Gambia: Barrow ya yi alkawarin kafa sabuwar kasa

Adama Barroow

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sakamakon zaben ya yiwa yawancin 'yan kasar Gambia dadi

Sabon zababben shugaban Gambia, Adama Barrow ya yi kira ga 'yan kasar da ke gudun hijira na siyasa a wasu ƙasashe saboda mulkin Yahyah Jammeh, da su koma kasar, don su taya shi gyara ta.

Ya kuma ce zai tabbatar da cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe, na sauya matakin da Shugaba Jammeh ya dauka na fitar da Gambia daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-wato ICC.

Mista Barrow ya kara da cewa, nasarar da aka samu a zaben 'yar manuniya ce da ke nuna mafarkin ';yan kasar na gab da zama gaskiya.

A wani mataki da ya kara tabbatar da zaman lafiya bayan sanar da sakamakon zaben, Shugaba Jameh ya kira Barrow ta wayar tarho, inda ya yi masa murna da fatan alheri da kuma alkawarin yin aiki tare dan mika mulki cikin ruwan sanyi.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi shugaba Jammeh da take hakkin 'yan luwadi, da 'yan jarida da kuma 'yan adawa.