Hikayata: Matsalar fyaɗe a kasar Hausa

Bayanan sauti

Hikayata: Matsalar fyaɗe a kasar Hausa

A ci gaba da karanto muku gajerun labaran da suka yi rawar-gani a gasar BBC Hausa ta farko ta rubutun kagaggen labari ta mata zalla, a yau za mu kawo muku karatun labari na biyu a cikin 12 da alkalan gasar suka ce sun cancanci yabo.

Kuma za mu karanto muku labarin "Hukunci" na Safiyyah Ummu Abdoul da Rufaida Omar.

Wannan labari ya mayar da hankali ne kan babbar matsalar nan ta yi wa kananan yara fyade, musamman a kasar Hausa.