Nuhu Ribadu da Farida Waziri na kai ruwa rana kan cin hanci

Farida Waziri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farida Waziri ta ce Ribadu ba shi da gaskiya

Tsofaffin shugabannin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'anna, EFCC, Nuhu Ribadu da Farida waziri sun zargi juna da hannu wajen aikata cin hanci da rashawa.

Wata sanarwa da Farida Waziri ta fitar ta ce ya kamata Malam Nuhu ya yi wa 'yan Najeriya bayani kan biliyoyin kudi da kadarorin da ya kwace daga wurin mutanen da ake zargi da cin hanci lokacin da yake shugabanci hukumar.

Tana mayar da martani ne kan zargin da Nuhu Ribadu ya yi mata a makon jiya cewa tana cikin mutanen da suka hana ruwa gudu a fafutikar da ya yi ta hukunta mutanen da ake zargi da cin hanci a kasar.

Tsofaffin manyan jami'an EFCC din dai ba sa jituwa da juna tun bayan da aka maye gurbin Nuhu Ribadu da Farida Waziri a hukumar ta EFCC, matakin da a wancan lokacin, 'yan kasar da dama ke yi wa kallo na yunkurin hana Ribadu hukunta wasu shafaffu da mai.

'Ta yi wa yaki da cin hanci illa'

A makon jiya ne Malam Nuhu Ribadu ya bayyana sunayen mutanen da ya ce sun yi masa kafar-ungulu wajen yaki da cin hanci a lokacin da yake shugabancin EFCC.

Ya yi wannan zargi ne a wurin wani taron shekara-shekara da cibiyar lauyoyi ta Joe Kyari Gadzama ta yi a Abuja.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cewarsa, Mrs Waziri "ta yi illa sosai ga EFCC ta yadda har yanzu hukumar bata farfado ba. Kafin ta zama shugaba babu wanda yake zargin jami'an hukumar da cin hanci. Amma ta kawo lauyoyi daga waje wadanda ta dora wa nauyin gudanar da shari'o'i masu muhimmanci lamarin da ya sa aka rika amfani da hukumar domin tatsar kudi a wurin masu laifi sannan a bar su."

Malam Ribadu ya ce daya daga cikin misalai na irin wannan matsala shi ne batun Halliburton wanda "bayan mun yi aiki tukuru mun kusa kai wa gaci sai ta mika batun ga wasu lauyoyi wadanda su kuma suka rika amfani da shi wajen neman kudi."

'Na gyara barnar da ya yi'

Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun Mrs Waziri, Omolara Oluremi, ta aike wa manema labarai ta ce akwai bukatar Ribadu "Ya nemi sakamakon binciken da aka gudanar kan shugabancinsa a EFCC domin nan gaba ya yi wa 'yan Najeriya kan biliyoyin kudi da kaddarorin da aka karbo daga wajen mutanen da ake zargi da cin hanci a lokacin shugabancinsa, inda babu wata shaidar da ke nuna cewa ya ajiye su."

"Ya kamata ya gode min saboda na gyara barnar da ya yi sakamaon kirkirar ofishin da zai kula da kaddarorin da aka kwato", in ji Farida Waziri.

Ta kara dsa cewa Nuhu Ribadu ba zai yi nasara ba a duk wani yunkuri da zai yi domin shafa mata kashin kaji.