'Boko Haram ta kashe mutum 1000 a jihar Diffa'

Sojoji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojoji sun sha alwashin murkushe Boko Haram

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe kusan mutum 1000 a Jamhuriyar Nijar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016.

Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar, CNDH ce ta bayyana hakan a wani sabon rahoto da ta fitar kan halin da kasar ke ciki.

Wani babban jami'in hukumar ya shaida wa BBC cewa mayakan Boko Haram "sun kashe mutum 995 - sojoji da fara-hula - a jihar Diffa kadai tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016. Rai ba karamin abu ba ne".

Ya kara da cewa jihohin Tahoa da Tillaberi ma sun yi fama da kashe-kashe a cikin shekaru biyu, inda wasu 'yan kungiyoyin 'yan ta'adda ke shiga daga Mali suna kai musu hare-hare.

Kungiyar Boko Haram da wasu kungiyoyin 'yan tawaye dai sun matsa kaimi wajen kai hare-hare a Jamhuriyar Nijar a shekarun baya bayan nan, musamman bayan fatattakar da ake yi musu daga Najeriya.

Hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa sun raba miliyoyin mutane daga muhallansu.

Kasashen yankin Tafkin Chadi, ciki har da Jamhuriyar ta Nijar, sun kafa runduna ta musamman domin murkushe kungiyar Boko Haram.