Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan 'yan gudun hijira

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Buhari ya ce kungiyoyin bayar da agaji ba sa aikinsu yadda ya kamata

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soki majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin bayar da agaji saboda "zuzuta" halin da 'yan gudun hijirar da Boko Hara suka kora daga gidajensu ke ciki.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce kungiyoyin suna kambama halin da 'yan gudun hijirar ke ciki ne da zummar samun kudi daga wajen gwamnatoci.

Ya bayar da sanarwar ce kwanaki kadan bayan majalisar ta dinkin duniya ta ce fiye da mutum 5m da Boko Haram ta raba da muhallansu na fuskantar hatsarin kamuwa mummunar yunwa.

A cewar Garba Shehu, "Mun damu kwarai kan kwan-gaba-kwan-bayan da irin wadannan kungiyoyi ke yi game da alkaluman da suke fitar wa kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki. Kwanan nan wata kungiyar majalisar dinkin duniya ta ce mutum 1000,000 za su mutu sakamakon yunwa a shekara mai zuwa. Daga bisani kuma wata kungiyar ta ce mutum 1m ne za su mutu."

Ya kara da cewa fitar da wadannan mabambantan alkaluma ta nuna cewa kungiyoyin ba su da cikakkiyar masaniya kan halin da 'yan gudun hijirar ke ciki.

Kakakin shugaban na Najeriya ya ce gwamnati na yin bakin kokarinta domin ganin ta sauwaka wa 'yan gudun hijirar halin da suke ciki.