Likitoci na yajin-aiki kan albashi a Kenya

Likitoci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Likitocin sun ce gwamnati ba ta cika alkawari ba

Likitoci a kasar Kenya sun shiga yajin-aiki bayan gwamnati ta ki cika musu alkawarin karin albashin da ta ce za ta yi musu.

Gwamnati da likitocin sun cimma matsaya cewa za a akra musu kashi 300 na albashin da suke karba shekara uku da suka wuce.

Yajin aikin ya kassara ayyukan da ake yi a asibitoci sama da 2000.

Gwamnatin dai ta ce bai kamata likitocin su shiga yajin aiki ba saboda umarnin da kotu ta ba su na dakatar da shiga yajin aiki zuwa karshen wata.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun fesa wa likitocin hayaki mai sanya kwalla da zummar korar su.