An birne mutane 51 da aka kashe a Uganda

uganda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fiye da mutane 80 ne aka kashe a rikicin, akasarinsu dogarawan sarki

A Uganda, an birne gawarwakin akalla mutane hamsin da daya, wadanda ba a gane ko su wanene ba, da aka kashe a rikici tsakanin jami'an tsaro da 'yan aware masu biyayya ga wani basarake a yankin Kasese dake yammacin kasar.

Hukumomin yankin sun ce babu wani da ya je domin karban gawarwakin.

Rahotanni sun ce wasu daga cikinsu sun kone sosai, har ba a iya gane su ba.

Fiye da mutane tamanin ne aka kashe a rikicin a makon jiya, akasarinsu kuma, dogarawan basaraken ne.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun zargi jami'an tsaron Uganda da kashe mutanen ba bisa ka'ida ba.

An tuhumi basaraken, Sarki Charles Mumbere da aikata laifin kisa.