Serie A: Roma ta doke Lazio 2-0

Kevin Strootman

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Roma ta ci bakwai daga cikin wasanninta tara na Serie A da ta yi a kwanan nan

Roma ta samu cigaba, inda ta zama ta biyu a bayan jagora a gasar Serie A Juventus da bambancin maki hudu bayan ta doke abokiyar hamayyarta Lazio 2-0.

Kevin Strootman ya ci Lazion, a minti na 64 bayan ya kwace kwallo daga Wallace lokacin da dan bayan Lazion ya yi kasassaba a cikin da'irarsu.

Cin kwallon ke da wuya sai alkalin wasa ya ba wa dan wasan Lazio Danilo Cataldi, wanda ba ya cikin wasa, jan kati (na kora) saboda ya ja rigar Strootman yayin da yake murnar kwallon da ya ci.

Radja Nainggolan ne ya jefa kwallo ta biyu a minti na 77, wadda ta zama cikammakin, da ta ba wa Roma maki ukunta.

Nasarar ta sa Roma ta sake komawa matsayi na biyu a teburin gasar ta Serie A, bayan da tun da farko AC Milan had ta yi mata tsallen-badake ta dare matsayin na biyu bayan ta doke Crotone 2-1.

Wannan shi ne karo na hudu a jere a gasar Serie A, da Roma ke yin nasara a kan abokiyar hamayyar tata ta birnin Rum Lazio.

Lazio ita ce ta biyar a tebur da maki 28, hudu kenan tsakaninta da Roma kuma takwas tsakaninta da Juventus ta daya mai maki 36, wadda ta ci Atalanta 3-1 ranar Asabar.

Filin ya kasance kusan fankanfayau domin dubban kujeru sun kasance ba kowa, saboda magoya bayan Roma da dama sun kaurace saboda korafin da suke yi kan irin matakan tsaron da ake dauka a filin.