Everton na son dawo da Wayne Rooney

Wayne Rooney

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wayne Rooney ya koma Manchester United daga Everton ne

Everton na son dawo da tsohon dan wasanta kyaftin Manchester United da Ingila, Wayne Rooney mai shekara 31, kungiyar kuma tana son raba dan wasan Holland Memphiss Depay mai shekara 22 da Old Trafford in ji jaridar Sunday Express

Haka kuma ana ganin Manchester United din za ta iya rasa matashin dan wasanta na gaba na Faransa Anthony Masiyal, mai shekara 20, zuwa Barcelona ko Real Madrid a kan wata yarjejeniya ta fam miliyan 60m.

Real Madrid din za ta yi musayarsa da dan wasanta na Colombia Yems Rodriguez kamar yadda jaridar Sun ta Lahadi ta labarto

To Jaridar Sunday Express kuwa ta ruwaito cewa Arsenal ta ce a shirye take ta dawo da tsohon dan wasanta, dan Spain Cesc Fabregas, mai shekara 29, daga Chelsea in ji Sunday Express

Liverpool kuwa za ta yi gwagwarmaya da zakarun Faransa Paris Saint German domin sayo matashin dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund dan Amurka Christian Pulisic, mai shekara 18 kamar yadda jaridar Bild ta ruwaito

Dan wasan Manchester United kuma na Ingila Jesse Lingard, mai shekara 23, na neman a kara masa kudi a yarjejeniyar da kungiyarsa ta gabatar masa ta biyansa fan dubu 60,a mako in ji Sunday Mirror

Har wayau dan wasan Arsenal kuma na Jamus Mesut Ozil, mai shekara 28, ya sake rura wutar rade-radin da ake yi cewa zai koma Real Madrid, a wannan karon an jiyo shi ne yana bayyana kocin kungiyar ta Spaniya Zinedine Zidane a matsayin gwarzonsa in ji jaridar Sun

Shi kuwa kocin Arsenal Arsene Venger kila zai nemi mai tsaron ragar kungiyar Crotone, dan Italiya, matashi Aniello Viscovo mai shekara 17, inda tuni Vengern ya fara tattaunawa da kungiyar ta Serie A in ji jaridar Tuttomercatoweb

Wani matashin dan italiyar da shi ma kila zai koma gasar Premier, wanda Chelsea ke shaawarsa shi ne dan wasan Inter Milan na gaba Andrea Pinamonti dan 17 in ji jaridar Sunday Mirror