"Sukar gwamnatin Buhari gyara kayanka ne"

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa na kokarin inganta rayuwar al'umma

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa na kokarin inganta rayuwar al'umma

A Najeriya, masu sharhi sun fara tsokaci kan sukar da fadar shugaban kasar ke fuskanta daga wasu muhimman mutane a kasar, wadanda a baya suka kasance cikin masu goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.

Suka na baya-bayan na dai ya fito ne daga Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II wanda ya soki manufofin gwamnati na tattalin arziki.

A baya ma wasu rahotanni sun ambato tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo yana nuna takaicinsa a kan yadda al'amura ke tafiya a kasar.

Dr. Abubakar Kari malami ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja, ya ce baya ga wasu masu fada aji da ke sukar gwamnati, akwai talakawa da dama dake korafi kan yadda gwamnati ke tafiya.

Ya kara da cewa talakawa sun zabi Muhammadu Buhari ne domin ya magance matsalolin da suka addabe su, kuma sukar da wasu ke yi wa gwamnatin sa tamkar gyara kayan ka ne.

"Buhari ya yi wa Sarkin Kano raddi"

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba daidai ba ne kalaman da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi cewa gwamnatinsa ta karbi N4.5tr, yana mai cewa N1.5tr ta karba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce, "Ina matukar mutunta mai martaba saboda shi sarkina ne; domin ni dan Kano ne. Amma akwai gyara a alkaluman da ya bayar.

Gaskiya ne gwamnati ta karbi kudi sosai daga babban bankin Najeriya, amma ba ta zarta ka'ida ba."

Shi dai Sarki Muhammadu Sanusi ya ce kudin da gwamnati ta karba daga babban bankin Najeriya sun ninka sau fiye da goma kan adadin da doka ta ba su umarni.

Sai dai Malam Garba Shehu ya kara da cewa, "Mu dauka maganar da ya fada gaskiya ce. Duk da haka gwamnati tana da kudin da ya zarta wanda ta karba a ajiye a asusun bai-daya. Kamar mutum ne mai asusun banki biyu; daya babu kudi, dayan akwai makudan kudi. Menene illar kwaso kudin daya asusun domin biyan bukatar al'umma?."

Kakakin na shugaban Najeriya ya ce ba zai yi wa Sarki Sanusi raddi kan adawar da yake yi ga kudirin gwamnati na karbi bashin $30bn, yana mai cewa ministar kudi za ta ba shi amsa.

A cewarsa, "A matsayi na na dan kasa zan so na sake karanta jawabinsa game da wannan batu. Amma ai za a karbo bashin ne domin yin ayyukan ci gaban kasar, cikinsu har da kafa layukan jirgin kasa da samar da hasken wutar lantarki."