Zaben Ghana: Ko wanene John Dramani Mahama?

John Dramani Mahama ke zaune a kujera a lokacin da ake rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a 2012

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

John Dramani Mahama ke zaune a kujera a lokacin da ake rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a 2012

Shugaban kasar mai ci yanzu John Dramani Mahama wanda ke neman wa`adin mulki na biyu na daga cikin `yan takara bakwai da za su fafata a zaben.

An haifi shugaban Ghana mai ci wato John Dramani Mahama ne a watan Nuwamban 1958, a lardin Bole Bamboi.

Ya riki mukamin mataimakin shugaban kasa daga shekara ta 2009 zuwa 2012, lokacin ya tsaya takara aka kuma zabe su da marigayi shugaba John Attah Mills a karkashin jam`iyyarsu ta NDC.

Kodayake a karshe kaddara ta sa ya dare karagar mulki a matsayin shugaban kasa, ana saura wata hudu wa`adin mulkinsu ya cika, sakamakon rasuwar magabacinsa, wato shugaba John Attah Mills.

Kuma a watan Disamban 2012 ne ya tsaya takara, kana ya samu nasarar zama zababben shugaban kasa a Ghana.

Mista Mahama kwararre ne a harkar sadarwa, masanin tarihi ne, harwayau marubuci ne.

An dade ana bubgawa da shi a jam`iyyar NDC, ksancewar ya zama dan majalisar dokokin Ghana a karkashin jam`iyyar har sau uku, wato daga 1997 zuwa 2009.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kuma yana aikin dan majalisar ne aka kara masa dawainiya, inda aka nada shi a matsayin Ministan Sadarwa, da mukamin Kakakin jam`iyya.

John Dramani Mahama ya kamala karatun digirinsa na farko a tarihi, da kuma babbar diploma a harkar sadarwa a jami`ar Legon ta Ghana.

Kazalika ya garzaya Moscow, inda ya yi karatun babbar Diploma a kimiyyar tunanin bil`adama da kuma zamantakewarsa.

Ya yi aiki da ofishin jakadancin Japan da ke Ghana, da kuma kungiyoyin farar-hula, ciki har da Plan International. Baya ga aikin koyarwar da ya yi a wasu makarantun Sakandaren Ghana.

Mahaifin Dramani Mahama , wato Emmanuel Adama Mahama attajirin manomi ne, kuma dan siyasa da ya yi nasa zamanin tare da madugun siyasar jumhuriya ta farko a Ghana, Dr Kwame Nkurumah.

Mista John Mahama dai na neman wa`adin mulki na biyu ne a matsayin zababben shugaban kasa.

Kuma zai kara da babban abokin hamayyarsa na jam`iyyar NPP, Nana Akufo Addo, wanda ya sha da-kyar a fafatawar da suka yi a zaben shugaban kasa a shekarar 2012.