Firai Ministan Italiya Matteo Renzi ya yi murabus

Mr Matteo Renzi ya ce ya dauki alhakin sakamakon zaben
Bayanan hoto,

Mr Matteo Renzi ya ce ya dauki alhakin sakamakon zaben

Firai ministan Italiya Matteo Renzi ya yi murabus bayan ya sha mummunan kaye a zaben raba-gardamar da aka gudanar kan sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar.

Sakamakon farko da kafafen yada labarai ya nuna kashi 42 zuwa kashi 46 sun kada kuri'ar amince wa da gyara kundin tsarin mulkin sabanin kashi 54 zuwa 58 da suka kada kuri'ar kin amince wa da gyare gyare.

Kashi 70 ne cikin 100 na masu kada kuri'a ne dai suka fito suka yi zaben raba gardamar.

A wani taron manema labarai, Mr Renzi, ya ce ya dauki alhakin sakamakon zaben kuma wadanda basa son gyaran daya nemi a yi a kundin tsarin mulkin kasar su suka fi rinjaye.

Daruruwan mutane ne suka yi ta murna a titunan birnin Rome, bayan da aka sanar da sakamakon zaben da kuma murabus din Matteo Renzi