Wane ne sabon shugaban kasar Ghana?

Nana Akufo-Addo

Asalin hoton, Getty Images

An haifi zababben shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo a ranar 29 ga watan Maris din 1944 a tsakiyar birnin Accra.

Kuma gidansu ne ya zama shedkwatar jam'iyyar siysa ta farko a Ghana wato UGCC.

Mahaifinsa da kawunsa da kakansa na daga cikin mutane shida da ake wa kallon wadanda suka kafa siyasa a Ghana, kuma ake muksu lakabin Big Six, ma'ana manya shida, cikinsu har da Kwame Nkuruma.

Nana Akufo-Addo kwararren lauya ne kuma dan siyasa, sannan hamshakin dan kasuwa. Ya jima yana tsayawa takarar shugagabancin kasar ta Ghana a matakai daban-daban.

A watan Oktoban 1998, ya nemi jam'iyyarsa ta NPP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar, to sai dai ya sha kasa a hannun takawaransa John Kufor, wanda ya zama shugaban kasar a shekarar 2000

Bayan jam'iyyar ta NPP ta kafa gwamnati, Nana Akuffo Addo ya zama babban lauyan gwamnatin kasar kuma ministan shari'a, daga baya kuma aka nada shi ministan harkokin kasashen waje.

To amma ya ajiye mukamin a shekarar 2007 domin tsayawa takarar shugabancin kasar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A zaben da aka yi a ranar 7 ga watan Disambar 2008 ya samu kuri'u mafiya rinjaye a zaben shugaban kasar, inda ya samu kaso 49 a kur'iun da aka kada, to sai dai hakan bai sa ya samu nasarar zama shugaban kasar ba, domin kuwa dokokin kasar Ghana sun tanadi cewa sai dan takara ya samu kaso hamsin sannan ya lashe zabe.

Tarihin siyasarsa

Murnar Nana Addo da magoya bayansa ta koma ciki a lokacin da aka je zagaye na biyu na zaben, yayin da abokin takararsa na jam'iyyar NDC John Atta Mills ya samu kaso 50 da 'yan kai, abinda ya bashi damar zama shugabana kasar.

Akufo-Addo ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2012, inda suka gwabza da shugaba mai ci John Mahamma na Jam'iyyar NDC.

Zaben dai ya janyo ce-ce ku-ce, daga karshe kotun kolin kasar ta yanke hukuncin da ya raba kan alkalanta, kuma aka tabbatarwa da Mahamma nasara.

Tun watan Maris na shekarar 2014, ya bayyana cewa zai tsaya takara a zaben na bana.

Don haka wannan ne karo na hudu da yake zawarcin kujerar shugaban kasar, kuma karo na biyu da za su fafata da abokin hamayyarsa shugaba mai ci John Mahama.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wannan shi ne karo na uku da Nana Akufo-Addo ke tsayawa takara

A shekarar 2014, Nana Akufo Addo shi ne shugaban tawagar masu sa ido a zaben shugaban a Africa ta Kudu.

A bangaren siyasa kuwa an jima ana damawa da shi. Ya taba zama babban sakataren wata kungiyar fautukar neman 'yanci da adalci mai suna Peoples movement for freedom and Justice, wacce ta jagoraci gangamin adawa da wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka so yin amfani da ita a lokacin, kan tsarin jam'iyya daya a kasar Ghana.

A 1992, Nana Akuffo Addo ya zama sakataren tsare-tsare na farko na jam'iyyar NPP. A 1995 kuwa ya jagoranci wata zanga-zangar nuna damuwa da halin matsalin tattalin arziki da aka fuskanta a lokacin shugaba Jerry Rawlings.

An zabe shi dan majalisar wakilai sai uku daga 1996 zuwa 2008.

Ta bangaren aiki kuwa Nana Akufo Addo ya yi aikin lauya na tsawon shekara biyar a Faransa.

Ya koma gida Ghana a 1979 inda suka hada gwiwa wajen kafa kamfanin aikin lauya. Kuma shi ne mutumin da ya kai wayar hannu Ghana ta yin amfani da wata sanayya da yake da ita da wani kamfani a Amurka.

Ta bangaren ilimi kuwa Nana Akufo-Addo ya yi makarantar primary ta Government Boys School ta Adabraka a Accra Gahana, Yayi karatunsa na sikandare da kuma makarantar gaba da sikandare a Ingila.

A shekarar 1962 Nana Addo ya koma Ghana domin koyarwa a makarantar sikandare, inda daga nan ya karanci tattalin arziki a jami'ar kasar Ghana, ya kuma kammala a 1967.

Daga nan ne kuma ya koma Birtaniya inda ya karanci aiki lauya, kuma ya zama lauya a Ingila a 1971.

Nana Addo Dankwa Akofu-Addo na da mata daya da 'yaya mata biyar da jikoki biyar.