Trump ya zargi China da boye darajar kudinta

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana ganin gwamnatin Mista Trump ba za ta yi kawance da wasu kasashen duniya ba, saboda banbancin ra'ayi

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da kakkausar lafazi a shafin sa na Twitter na sukar manufofin kasar China.

Mr Trump ya zargi China da yin coge kan batun daya shafi darajar kudinta, lamarin dake shafar ayyuka a Amurka da kuma amfani da karfi wajen gina wuraren ayyuka na soji a teku dake kudancin Chinan.

Sukar da Mr Trump din ke yi dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da Chinan ta rika sukar zababben shugaban saboda tattaunawar da ya yi da shugaban kasar Taiwan, abun da ya ke sabanin manufofin kasashen waje da aka san Amurka akai.

Tun da farko sakataren harkokin wajen Amurkar John Kerry, ya shawarci 'yan kwamitin karbar mulki na Mr Trump da su rika tuntubar ma'aikatar harkokin wajen Amurkar kafin magana da shugabannin wasu kasashen duniya.