Saudiyya ta yanke wa Iraniyawa hukuncin kisa saboda leken asiri

Rouhani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukuncin zai taba ran Iran

Wata kotu a kasar Saudiyya ta yanke wa Iraniyawa 15 hukuncin kisa saboda kama su da laifin leken asiri.

Mutanen na cikin mutum 30, yawancinsu 'yan Shia na kasar Saudiyya, wadanda aka tsare shekara uku da suka wuce sannan aka fara yi musu shari'a a watan Fabrairu.

An kama su da laifin kafa wata kungiya da ke yi wa Iran leken asiri da zummar yin kafar-ungulu da kuma tayar da zaune tsaye a kasar ta Saudiyya.

An yanke wa 15 daga cikin su hukunci dauri, yayin da aka sallami mutum biyu saboda ba a same su da laifi ba.

Kafofin watsa labaran Saudiyya sun ce akasarin mutanen tsofaffin sojoji ne, wadanda ake zargi da bai wa Iran bayanan sirrin Saudiyya.

Ana kallon wannan hukunci a matsayin wani batu da zai kara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen biyu.