Zaha: Za a yi ja-in-ja Ingila da Ivory Coast

Wlfried Zaha

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wlfried Zaha ya yi wa Ingila wasanni a gasar 'yan kasa da shekara 20.

Ga alama za a yi ja-in-ja tsakanin Ingila da Ivory Coast a kan dan wasan gefe na Crystal Palace, Wilfried Zaha, kan wadda zai yi wa wasa a matakin kasa da kasa.

A makon da ya wuce ne, Zaha mai shekara 24, ya ce ya gabatar da takardun neman bukatar hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta ba shi damar ya koma yi wa kasarsa ta haihuwa, Ivory Coast wasa.

Daga nan ne sai kocin Ingila Gareth Southgate ya ce sam ba za ta sabu ba, domin zai yi duk abin da zai iya yi, ya shawo kan, dan wasan da kansa, domin ya sauya shawara.

To amma kuma Malick Tohe, mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Ivory Coast, ya ce ai tuni sun kama hanyar kammala daukar dan wasan.