Hukumar hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasa ta je Kenya

Kenya athletes
Bayanan hoto,

An dade kafin hukumar hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta Kenya ta bi ka'idojin ta duniya

A ranar Litinin ne wasu jami'an hukumar hana amfani da abubuwa masu kara kuzari a wasanni ta duniya, suka hallara a Kenya, domin duba yadda takwarar hukumar ta kasar ke aiki.

A yayin ziyarar za su duba tare da bibiyar yadda tsarin aikin hukumar ta Kenya ta hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasannin yake.

A watan Janairun 2015 ne aka kafa hukumar ta Kenya, amma kuma sai a watan Yuni na wannan shekara ta 2016 ne, bayan Kenyan ta bi ka'idojin hukumar ta duniya, dokokin hukumar ta Kenya suka fara aiki.

Sai dai an yi shakkun gaskiyar hukumar ta Kenya sakamakon kama wasu jami'an wasanninta biyu da hannu a badakalar shan abubuwan kara kuzari a gasar Olympics ta Rio, kuma aka kora su gida daga gasar ta Brazil.