Zaben Ghana: ECOWAS ta tura wakilanta

Tawagar ECOWAS ta kunshi mutum 94 da za su sa ido a zaben Ghana
Bayanan hoto,

Tawagar ECOWAS ta kunshi mutum 94 da za su sa ido a zaben Ghana

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, ECOWAS ko CEDAO ta tura tawagar wakilanta da za su sa ido a kan zaben shugaban kasar da za a yi a Ghana a ranar Laraba.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce tsohon shugaban rikon-kwarya na gwamnatin Liberia, Amos Sawyer ne zai jagoranci tawagar.

ECOWAS ta bayyana cewa tawagar wakilan nata za ta kunshi mutum 94, wadanda za su yi aikin sa idon a zaben shugaban kasar don tabbatar da cewa an bi ka`ida tare da kamanta adalci da gaskiya a zaben.

Kungiyar ta ce ta raba tawagar zuwa gida biyu, wato 80 daga ciki za su yi aikin sa-ido ne na gajeren zango, yayin da 14 hudu kuma za su aikin ganin-kwa-kwab.

Masu sa-ido na gajeren zangon, a cewar sanarwar an tattaro su ne daga kungiyoyin farar-hula da wakilan hukumomin zaben na kasashen da ke shiyyar Afirka ta yamma da jakadun da ke aiki da kungiyar ta ECOWAS, da kuma ayarin masu sa-ido daga cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Kofi Anan.

Tun a ranar 27 ga watan Nuwamban da ya wuce ne tawagar masu sa-ido, rukunin `yan ganin kwak-wab mai mutum 14 ta isa birnin Accra wadanda galibinsu kwararru ne ta fuskar tsaro da aikin zabe da siyasa da kuma dokokin kasa da kasa.

Ana sa ran za a rarraba masu sa idon zuwa dukkan lardunan Ghana guda Goma gabannin fara zabe da kuma sauran abubuwan da ka iya biyo baya.

Kazalika a karshen zaben, tawagar za ta gabatar da rahotonta a kan yadda zaben ya gudana tare da ba da shawarwarin da suka dace.

A ranar Laraba ne za a gudanar da zaben shugaban kasar wanda mutum

'yan takara bakwai ne zasu fafata a zaben shugaban kasar ciki har da shugaba mai ci.

Kazalika za a gudanar da zaben `yan majalisar dokokin kasar mai kujeru 275.

Tuni dai kungiyar ECOWAS din ta bukaci dukkan `yan takara da shugabannin siyasa da kuma magoya bayansu da su kai zuciya nesa don tabbatar ganin an yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.