Nigeria ta haramta shigo da motoci ta iyakokinta

Shugaban hukumar kwastan ta Nigeria Kanar Hamid Ali mai ritaya

Asalin hoton, NIGERIA CUSTOMS

Bayanan hoto,

Shugaban hukumar kwastan ta Nigeria Kanar Hamid Ali mai ritaya

Gwamnatin Nigeria ta haramta shigar da motoci cikin kasar ta kan iyakokinta na kasa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar hana fasakauri ta kasar ta fitar inda ta ce dokar ba za ta fara aiki ba sai ranar daya ga watan Janairu mai zuwa.

Hukumar ta ce haramcin ya shafi shigowa da sababbi da kuma tsofaffin motoci, sai dai bai shafi shigar da motoci zuwa kasar ta ruwa ba.

Wannnan mataki na haramcin shigar da motocin ya zo ne bayan da gwamnatin ta haramta shigar da shinkafa ta bakin iyakokin kasar tun daga watan Afrilun 2016.

Hukumar hana fasakaurin ta kuma shawarci maso shigowa da motoci ta kasa da su gaggauta kwashe motocin da suka shigo dasu a ruwa amma kuma suke wasu tashoshin jiragen ruwa na wasu kasashe makwabta.