Miss Park na cikin tsak mai wuya

Park Guen-hye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Badakalar da aminiyar shugaba Park ke ciki ta janyo cece-kuce a kasar

Ana yiwa manyan 'yan kasuwa a kasar Koriya ta Kudu tambayoyi da ake watsawa ta gidajen talbijin dangane da badakalar da ta dabaibaiye shugabar kasar Park Geun-hye.

Shugabannin kamfanin lataroni na Samsung dana kamfanin kera motocin Hyundai, na daga cikin wadanda suka bada shaida a gaban kwamitin Majalisar dokokin kasar.

Ana dai tambayar su ne akan ko sun fuskanci matsin lamba daga babbar kawar ta Choi Soon-sil, akan su bada gudummuwar miliyoyin daloli ga wasu gidauniya guda biyu domin samun alfarma daga gwamnati.

Shugaba Park dai na fuskantar kada kuri'ar tsigeta daga kan mulki kan batu a ranar juma'a mai zuwa.

Wakilin BBC ya ce kwamitin Majalisar bai da iko na yin hukunci amma shugaban kwamitin ya ce zaman wata dama ce ta neman gafarar al'umma.