Ana bankwana da fitacciyar 'yar siyasa Jayalalitha

Marigayiya Jayalalitha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fitacciyar 'yar siyasar ta bada gudummawa a ci gaban siyasar kasar India

Dubban jama'a ne a birnin Chennai dake kudancin Indiya suka yi dogayen layuka domin yin bankwana da fitacciyar 'yar siyasar nan ta kasar Jayalalitha, wacce ta mutu ranar Litini.

An dai lullube gawarta da tutar kasar inda aka ajiye a gaban wani dakin taro da jama'a ke zuwa, yayin da aka aike da jami'an 'yan sanda masu yawa zuwa wurin.

Firai ministan kasar Narendra Modi, ya ce mutuwar Ja-ya-la-li-tha sakamakon bugun zuciya tana da shekaru 68 ta bar wagegen gibi a fagen siyasar kasar.

A shekarar 2014 ne dai aka tuhumeta da laifin cin hanci, sai dai daga bisani an dawo da ita kan mukamin minista bayan an wanke ta daga zarge zargen da aka yi mata.