Yau za a fara zaman shari'ar kwamandan LRA Dominic Ongwen

Kwamandan LRA Dominic Ongwen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana tuhumarsa da laifukan take hakkin bil'adam, da yi wa mata fyade, da kisan gilla, da tursasa matasa shiga kungiyar masu dauke da makamai

Nan gaba a yau ne za a fara shari'ar tsohon kwamandan kungiyar 'yan tawaye ta LRA Dominic Ongwen, a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague wato ICC.

Kungiyar 'yan tawayen LRA dai ta shafe kusan shekaru 20 ta na gudanar da ayyukanta a arewacin kasar Uganda.

A baya dai kungiyar ta yi kaurin suna wajen kona wasu kauyukan kasar, da sace mata da kuma maza matasa, da kona kauyuka.

Ana zargin Mista Ongwen da aikata laifukan take hakkin bil'adama, ciki har da yiwa mata fyade, kisan gilla, da tursasa matasa shiga kungiyar masu dauke da makamai, da sace mata, da kona kauyuka da sauransu.

A nasa bangaren Mista Ongwen, yace shi ma wata kungiyar 'yan tawaye ce ta sace shi a lokacin da yake shekara 14 a kan hanyarsa ta zuwa makaranta.

Ya dade ya na fadi tashi a cikin kungiyar har zuwa girmansa, da samun nasarar rike mukamin kwamandan kungiyar LRA na runduna ta hudu, mai kula da dabarun yaki.

Shari'ar dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu shugabannin kasashen Afurka ke cewa za su fice daga kotun ta ICC.

A baya kuma gwamnatin kasar Ugandan ta zargi ICC da nuna wariya, ta hanyar gurfanar da 'yan Afurka kadai a gaban ta.