An ba wa kungiyar Chapecoense kofi

Family and supporters paying tribute to the players

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Iyalai da magoya baya na ci gaba da jimami da yaba wa 'yan wasan da suka mutu a hadarin jirgin

Hukumar kwallon kafa ta Latin Amurka ta ba wa kungiyar kwallon kafa ta Brazil Chapecoense kofin Copa Sudamericana bayan da yawancin 'yan wasanta suka mutu a hadarin jirgin sama lokacin za su je wasan karshe na cin kofin.

Mutun 71 ciki har da 'yan wasa biyar da ma'aikata ne suka mutu a hadarin a ranar Litinin ta makon da ya wuce 28 ga watan Nuwamba, a kan hanyarsu ta zuwa wasan farko na karshen.

Abokan karawarsu a wasan na karshe, kungiyar Atletico Nacional ta kasar Colombia, wadda ta ce a bawa kungiyar kofin, ita ma an ba ta takardar yabo ta shedar wasa cikin lumana.

Za a ba wa Chapecoense kudi dala miliyan biyu, kudin da ake ba wa kungiyar da ta dauki kofin, sannan kuma Atletico Nacional za ta samu dala mliyan daya.